Wata majiyar kai agaji a birnin na Bangazi ta ce a wannan sabon yunkuri da ‘yan bindigar suka sake kaiwa kimanin Mutane 30 sun samu mumunan rauni daga cikinsu.
Daga nashi waje Sakar Jarushi wani komandan sojojin Sama na kasar ya tabbatar da wannan labari, sannan ya ce har yanzu babban filin tashi da sabka na jiragen saman birnin Bangazi na kalkashin ikon Sojoji masu biyayya ga khalifa haftar tsohon janar mai ritaya. ABNA